Rundunar hadin guiwa ta yan
shi’a ta kaddamar da wani hari a yammacin garin Mosul na Iraki a
yunkurinta na korar yan kungiyar ISIS daga garin wanada shine birni na biyu da
ke karkashin ikon kungiyar.
Rundunar
da akafi sani da "Popular Mobilization
Units" a kwanakin baya dai ba ta bada wani gudumawa ba a sauran yakunan da su ka gabata,
amma fa harin da takai a yau Asabar ya janyo hankalin masu hasashe inada suke
ganin nangaba zata tabuka abun azo agani a sauran yakin kwato sauran birane dake hannun ta ISIS.
Garin na
Mosul dai na tsakanin iyakar kasar
Siriya da Iraki kuma shine birni na biyu da ya rage a hannun kunkiyar ISIS a
halin yanzu .