Labaran da suka fi Jan hankali

Friday, 25 October 2019

Dan bautan kasa ya kashe yaro dan shekara 9 har lahira a kano.

A jiya ne wani dan bautan kasa ya kashe yaro dan shekara 9 a garin Bebeji dake jahar kano.


Lamarin yafaru ne yayinda yaron ya shiga gidan na yan bautan kasan domin daukan yayan itace na ambulera, Hasan dan shekara 9 ya hadu da ajalinsa ne yayinda daya daga cikin yan bautan kasan mai suna Gibson Akinwumi Peter dan jahar Plateau ya iske shi a gidan inda nan take yahaushi da duka baji ba gani, bayan ya hadashi da gini inji shidun gani da ido nan take jini yafara fita daga hanchin yaron, bayan an garzaya da yaron asibiti na take yace gagarinku.

Mahaifin yaron malam Sule ya bayyana mana cewa, su yan bautan kasan ne suka bude ma yaran hanya shigan gidan ta inda suke aikan su sai su basu yayan itacen, yayinda idan basanan yaran ke shiga gidan domin ciran amburelan da kansu,

Hakazalika mahaifin yaron ya tabbatar mana da cewa tuni yansanda suka chapke mista Gibson inda suka garzaya dashi ofishin C. I. D dake cikin garin Kano.

Hakazalika munsamu labarin cewa Gwamna Ganduje ya kai gaisuwar ta'aziya ga iyayen yaron yau da yamma a garin na Bebeji. 

No comments:

Post a Comment