-Sannan Kuma, Ƙungiyar Ta Yi Kira Ga Marubuta Na Arewa Da Su Cigaba Da Rubuce-Rubuce Kan Wannan Batu Har Zuwa Lokacin Da Za A Hukunta Masu Wannan Ɗanyen Aiki.
Yau Litinin, 14 ga watan Octoba, 2019.
Ƙungiyar marubuta ƴan Arewa masu amfani da yanar gizo-gizo, wato (Association Of Arewa Bloggers) ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Bashir Abdullahi El-bash, ta bayyana takaicinta da kuma jimami matuƙa kan labarin da ta samu na yadda wasu Inyamurai su ke satar yara ƙanana a Jihar Kano su ke kuma kai zuwa Jihar Anambra su na sayar da su tamkar bayi tare da sauya musu addini, harshe, da kuma al'adu da ɗabi'un da su ka gada iyaye da kakanni.
Wanda hakan ya ci karo da tsarin dokokin ƙasa da kuma haƙƙi da ƴancin ɗan adam a duk Duniya ma gaba ɗaya, ba wai a Nageriya kawai ba. Kuma wannan ƙungiya ba za ta zuba ido ta ƙyale wannan batu ba, da yardar Allah za ta ɗauki dukkan wasu matakan da su ka dace tun daga kan rubuce-rubuce a (Social Media) da sauran kafafen watsa labarai har zuwa kan isar da koke da ƙore-ƙore kan wannan batu zuwa ga masu ruwa da tsaki a fannoni daban-daban domin tabbatar da hukunci na daidai ga waɗannan mutane masu satar mana yara.
Sanin kowa ne a shekarar (2016) akwai wani ɗan Arewa da ake kira da Yunusa Yello wanda ya taho da wata budurwa ƴar Kudu mai bin tafarkin addinin kiristanci, mai suna Ese Oruru zuwa Arewa domin raya Sunnar ma'aiki (S.A.W), amma ƴan uwanta ƴan kudu su ka yi ca akansa kamar sa cinye shi nama ɗanye da sunan wai ya gudo musu da yariya.
Haka manya Jaridun ƙasar nan da sauran gidajen yaɗa labarai su ka yi ta zuzuta abun har sai da ta kai Yello da zaman gidan Yari. Duk kuwa da cewar Yello ba sato yarinyar ya yi ba, da yardarta su ka taho, kuma ba yarinya ba ce ƙarama da hankalinta, wadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya ba ta damar zaɓin wurin zama da kuma shiga duk nau'in addinin da ta ke so.
Amma su waɗannan yara sace su aka yi a gaban iyayensu, wanda hakan ya ci karo da tanade-tanaden dokokin ƙasa da na hukumomin kare haƙƙin ɗan adam a Duniya gaba ɗaya. Sannan cin zarafi ne da wulaƙanta yara gami da tozartar su, haɗe da shiga haƙƙin iyayensu da ƴan uwa da kuma dangi gaba ɗaya.
Saboda haka ƙungiyar (Arewa Bloggers), mu na kira da babbbar murya ga marubuta ƴan Arewa gaba ɗaya masu amfani da yanar gizo-gizo da a cigaba da tattauna wannan batu a har zuwa lokacin da za a yi wa wannan yara da iyayensu da kuma Jihar Kano da Arewa gaba ɗaya adalci.
Domin a bisa ga dukkan alamu ba wannan ne karon farko ba, sun jima su na yi, sai a wannan karo ne dai Allah ya tona musu asiri. Dan haka ba za mu bari hakan ta cigaba da faruwa ba da yardan Allah.

No comments:
Post a Comment