Labaran da suka fi Jan hankali

Thursday, 24 October 2019

Lallai kaine gwaska!!! Kudin Nanaye yayi Albarka.


Jinjina ta musamman ga jarumi Adam A Zango da akafi sani da Usher,

Ilimi shine kashin bayan cigaban duk wata kasa da al'uma a doron duniya, kana sanin darajar ilimi shine ke sanyawa mutum tausayin wadanda suke son yin karatu amma talauci ko maraici ya hanasu samu wannan gagarumin dama,


Samun masu zuciya cikin jaruman arewa irin na Adam zango abun murnane, domin kasancewansa sabon abu a wurin mu, akuwai jaruman da suka fisa kudi amma hankalisu bai karkata kan wannan abun alkhairin ba,

Jaruman finafina bollywood sunjima suna taimakon marasa karfi a bangarori daban daban na rayuwa, irinsu Yuvraj Singh, Sharaddah Kapoor kai akwanannan ma akuwai wani tauraron danwasan kwallon 🏏cricket  🇮🇳 Sachin Tendulkar ya dauki nauyin karatun yara 200 da kudin sa,

Yau gashi muma a Arewa munfara samun irinsu Adam Zango, yadauki zuzurutun kudi sama da ₦40 million don daukan nauyin karatun yaran talakawa da marayu,

Allah yasa abun yazama gasa a tsakanin su mu farajin sun Sarki Ali Nuhu sun dau nauyin mutum 500,

Alhamdulillah kudin Nanaye yayi Albarka😁😁😁

No comments:

Post a Comment