Labaran da suka fi Jan hankali

Monday, 14 October 2019

Arewa da ya'ya'nta Akuwai matsala


Arewa da ya'ya'nta Akuwai matsala.

Ya bayyana karara cewa wasu yan kudu sun sace yara a kano sun chanja musu suna da addini yayinda Umarul Faruk ya koma Emanuel 😥😰😭



Wannan bama shine abun dubawa illa yadda manyan kafafen watsa labaru na kudancin kasanna sukayi wa labarin gum! amma ba laifin su bane laifin mu yan arewa ne da haryanzu mun kasa kafa gidajen watsa labaru ingatattu wanda zasuyi gogayya da tasu.


Abun takaicin ma shine mu yan arewa bamu damu da kasancewar mu a hakan ba domin kuwa yanzu kusan kowani gida kashiga tashar da a kafi kallo da tinkaho da ita ta arewa itace Arewa24 wanda a tunanina har abada bazata taba isar da sakon yan Arewa ga idon duniya.

a lokacinda wani bakane ya sato zuciyar wata yar kudu kwanakin baya tashar ChannelsTv TVCnews sunyi ta yayata wannan labarin inda yakai har duniya ta yarda budurwannan sato ta yayi kana ya tirsasa mata shiga musulunci.

Idan bamu gyara ba toh haka za'a ci gaba domin yanzu ta hanyar kafafen watsa labarai ake cin al'umma da yaki.

Allah ya kyauta!

No comments:

Post a Comment