Labaran da suka fi Jan hankali

Thursday, 30 August 2018

KASAR AMURKA CE TA 1 A DUNIYA A HARE-HAREN YAN BINDIGA DADI.

Yayinda hare-haren yan bindiga dadi ke lakume ran mutum 250,000 a kowani shekara,
wani bincike da kungiyar likitoti ta Amurka ya nuna cewa kasar ce  tazo ta farko cikin jerin kasashe 6 da wannan bala'i ya fi addaba a duniya.
binciken da aka wallafa sakamakon nashi a wannan makon ya nuna cewa kasar Brazil, Colombia, Guatemala, Mexico, da Venezuela, sune na gaba-gaba biyo bayan Amurka.
Binciken ya bada dalilai cewa yawan harkalla da safarar miyagun kwayoyi da sukayi kamari a wadannan kasashe shine ya haddasa wannan mummunan bala'in.
ALKALUMAN BINCHIKEN
mutane da suka mutu a Amurka kawai yakai 35,800  a shekarun 1990 inda adadin yakai 37,200  a shakarar 2016.

No comments:

Post a Comment