Labaran da suka fi Jan hankali

Tuesday, 28 August 2018

NAJERIYA NA BUKATAR SHUGABA JAJIRCECCE MAI AMANA BA MAI KAWARIN JIKI BA.


Tsohon shugaban hukumar zabe na kasa ferfesa Attahiru jega yace najeriya na bukatar shugaba jajircecce da amana ba mai karfin jiki ba,
domin shugaba mai nuna karfin mulki zai kare ne a lalata ma'aikatu a maimakon daidaitasu.
Tsohon shugaban hukumar zaben ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron shekara na kungiyar lauyoyi na Najeriya karo na 58 a Abuja.

ya kara da cewa ''Abunda muke bukata a yanzu shine jajartattun shuwagabanni masu fada da cikawa da kokarin yin ayyuka managarta, sabi da haka ya kamata mu kula sosai domin bana ganin shugaba mai nuna karfin mulki zai taimaka''.


No comments:

Post a Comment