A karon farko majalisar dinkin duniya tafitar da wani rahoto inda ta ce dole ne a binciki manyan jami'an soji na kasar Myammar bisa kisan kare -dangi da keta hakkin dan adam akan musulmi a jahar Rakhine dama wasu sassan kasar.
Rahoton yana cewa matakan da hukumomin "sun saba kwarai da gaske da batun da suke yi cewa 'yan kabilar Rohingya na barazana ga tsaro"
Kazalika rahoton ya bayyana sunan manyan jami'an soji 6 da yakamata dole a mika sunayensu ga ICC kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, haka zalika shugabar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, bata tsira ba inda rahoton ya chachaketa saboda rashin tsoma baki domin a daina kashe Musulmi.
Tarihi yanuna cewa musulmi yan kabilar Rohinja sun dade suna fuskantar kisa, chin mutunchi, keyta- hakkin bil'adama da chin-zarafi iri-iri daga gun yan addinin Budah na kasar dama ja'mi'an tsaro.
Akalla Musulmi 700,000 na kabilar Rohingya suka fice daga Myanmar inda suka nufi kasar Bangladesh. ayayinda aka kashe sama da 10,000.





No comments:
Post a Comment