Labaran da suka fi Jan hankali

Wednesday, 29 August 2018

YAN SANDA A LEGAS SUNYI ABUN GANI A YABA

Rundunar yan sanda a Legas ta kama wasu mutane 57 da ake zargin yan luwadi ne.
mutanen dubun su ya cika ne yayinda suke
bikin shigar da wasu matasa cikin kungiyar tasu a wani Otel a garin na Legas.
Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Lagos Edgal Imohimi ya shaida wa manema labarai cewa, an kama mutanen ne bayan wasu bayanan sirri da rundunar ta samu.
To sai dai wasu daga cikin wadanda lamarin ya ritsa dasu sun shaidawa kanfanin dillancin labarun Najeriya NAN cewa su rakiya da cin Abinci ne kawai ya kawosu yayin da wasu sukace yan rawa ne su.
Kakakin rundunar yansandan na Legas Chike Godwin Oti, ya shaidawa BBC cewa wadanda suka damken sun samesu da haramtattun ababe kamar Tramado, Tabar- wiki, da sauransu, ya kuma kara da cewa da zaran sun gama bincike zasu turasu gaban Kotu.
Kasar Najeriya dai ta haramta luwadi, kuma duk wanda aka kama da laifin zai sha daurin shekara 14 a magarkama.

No comments:

Post a Comment