Labaran da suka fi Jan hankali

Saturday, 6 August 2016

Auren da baya bukatan sadaki, Ka Auri kanwata na Auri kanwarka Idan ka saki kanwata Nima Dole na Saki kanwarka Koda Muna zaman Lafiya.

Asanin Kowa Aure A adinin Islama dama na kirista Baya yiyuwa Sai da sadaki(Islama) ko kuma Dukiya(Kirista), Amma a shi auren Musaya Wanda ake kira da "shigar" Abun ba haka yake ba,
Shi Aurene na Al'ada Wanda ake
musayar Kanne Mata tsakanin yayu maza na gidaje 2, ma'ana ni idan  ina da kanwa  mace sai na nemo wani ko cikin abokaina ko makwabta mai kanwa sai  muyi  musaya.
Amma fa Shi wannan aure dorewarsa  sai kowannen Ku ya zauna lafiya da matarsa, ma'ana idan ka saki kanwa ta dole Nasaki kanwar ka koda muna zaman lafiya da taka kanwar.
Shidai wannan auren na Shigar ya shahara Ne a kasar Yemen, duk da cewa malamai na fadakar wa da a daina yin wannan aure na al'ada domin ya sabawa karantarwar addini, Ammafa haryanzu Anayinsa a Kauyukan Kasar Yemen, kuma masu yin na ganin cewa shine aure mafi sauki ga Talakawan kasar.

No comments:

Post a Comment