Labaran da suka fi Jan hankali

Friday, 5 August 2016

Dogara Na Neman Taimakon Buhari Kan Badakalar kasafin Kudi

Shugabn majalisar wakilan Najeriya yau zai Gana da shugaba Buhari kan Badakalar kasafin kudin da ya janyo CeCe kuce a zauren majalisar.

Jaridar premiumtimes ta ruwaito cewa shugaban majalisar ya nemi ganawa da shugaba Buhari Ne domin ya fede masa biri har wutsiya dangane da batun Badakalar kasafin kudin da ya dabaibaye majalisar da kansa, a tunaninsa shugaba Buhari zai yarda da zargin da abokin fadan nasa wato jibirilla ya ke masa.
Idan Baku manta ba dai yau kusan kwanaki uku kenan da shugaban majalisar da shi Jibrilla suka amsa gayyatar uwar jam'iya (APC) da tayi musu a Abuja domin sasanta Lamarin.

No comments:

Post a Comment