Labaran da suka fi Jan hankali

Wednesday, 3 August 2016

Shawari 50 ga mai neman Jin dadin aure daga bakin Shiek Aminu Ibrahim daurawa.
1 mai ya sa kayi aure
2 Ka zabi mai addini
3 Mai kaunar Ka
4 Mai haihuwa
5 Mai saukin hali

6 Mai Tarbiyya
7 Mai kamewa
8 Ka ni sanci mai hali 6 mai mita.mai gori.
Mai hange hange. Mai Kwadayi. Mai rainuwa.
9 Mai hakuri
10 Daidai da kai.
11 Ra'ayinku yazo daya
12 Ka binciki halayanta da kyau
13 Ka bayyana mata manufofinka.
14 karbar kaddara yadda tazo. Bayan kayi iya
yinka
15 kada kayiwa matar da zaka aura karya
16 Ka bincika lafiyar juna akawai ciyukan da
ake dauka.
17 Ka gane kuna da banbanci da matar Ka.
18 Ka dinka yiwa matar Ka kyautar ba zata.
19 idan tayi kwalliya ko girki Ka yaba mata.
20 Ka bata lokaci na hira da tattaunawa
21 Ka dinka tafiya da ita lokaci Bayan lakaci.
22 Ka dinka jaddada soyayya da kalamai
masu dadi.
23 kada Ka kuskura Ka sabawa Allah Don Ka
farantawa matarka.
24 Ka zama mai juriya da shanye kananan
matsaloli.
25 Ka ginka girmamma raayin matarka.
26 kada Ka zama mai kama karya
27 mace sai hakuri.
28 Ka dena kangama kananan abubuwa.
29 Ka dena gwasile matar Ka ko kushe ta .
30 Ka kula da tsaftar kanka mata basason
miji kazami
31 kanka dinka ado da kwalliya
32 Banda cin Amanar aure.
33 Ka kiyayi saurin fushi
34 Banda duka da zagi da cin fuska
35 Ka dena lissafa abinda ya wuce
36 Ka zauna da matarka a matsayin miji
kawai ba malami ko mai kudi ko mai mulki
ba.
37 Ka dauki aure a matsayin ibada.
38 kada Ka dinka auna rayuwar Ka ta aure da
wani.
39 Ka dena gayawa mutane rayuwar Ka da
iyalanka.
40 Ka nisanci zargi sai da hujja mai karfi
41 kada Ka yankewa matar Ka hukunci da
zato ko jita jita
42 Ka dena gaggawar furta kalmar saki
43 komai yana iya cangawa Don haka kada
Ka nunawa matarka rayuwa iri daya .
44 kada Ka zargi matarka akan wasu
abubuwa da suke faruwa. Wasu kaine dalilin
faruwar su
45 kar Ka zama kullum kada gida Ka dinka
basu iska
46 Munin alakar Ka da Allah tana shafar
auranka .
47 kaba matarka hakuri idan Ka muzanta
mata.
48 Ka dinka tausawa mata
49 Rayuwa jarrabawa ce. Ka lura da wannan
50 Ka yawaita zikri da addua da karatun
Alkurani mai girma.

No comments:

Post a Comment