Labaran da suka fi Jan hankali

Wednesday, 3 August 2016

Hukumar kula da zirga zirgan jiragen kasa ta Nigeria ta gargadi sojoji da yan sanda

Hukumar kula da zirga zirgan jiragen kasa ta Nigeria ta gargadi hukumomin tsaro da duk wani mai hawa jirgin kasa batare da ya sayi tikiti ba.

Hukumar ta yi wannan gargadin Ne ta bakin shugabanta mai kula da yankin Lagos/Ogun Jerry Ouche a yayin hira da kamfanin dillanci labarun kasar NAN yau a Legas.
Shugaban yace babu wani Wanda aka ware ya hau jirgin ba tare da ya sayi tikiti ba.

No comments:

Post a Comment