Labaran da suka fi Jan hankali

Wednesday, 3 August 2016

Duniya Makaranta data shiek Aminu Ibrahim Daurawa

*DUNIYA MAKARANTA*
1.Hakuri iri biyu ne: hakurin abinda ka ke so idan ba ka same shi ba, da hakurin abinda ba ka so idan ya same ka.
2. Duk kofar da ka ganta a rufe tana da mabudi. Kada ka saki baki kana jiranta ta bude da kanta.
3. Duk wanda ya yabe ka da karya wata rana sai ya zage ka.
4. Komai a duniya yana da mabudi. Mabudin ilimi shine tambaya, mabudin nasara hakuri, mabudin arziki tsoran Allah, mabudin zaman lafiya adalci da gaskiya.
5. Hattara da mabudai guda uku:

A. Fushi, mabudin azaba.
B. Tsoro, mabudin fitina.
C. Kwadayi, mabudin wahala
6. Ba zaka taba sauka a tashar nasara ba sai ka hau motar hakuri da jajircewa da sadaukarwa.
7. Zuciyar ka ita ce adireshin ka. Harshen ka shine ma'aunin ka. Gyara Zuciyar ka sannan ka kula da harshen ka.
8. Kada ka damu da masu kulla maka sharri, duk iya kokarin su ba su wuce zartar da kaddarar Allah a kan ka.
9. Mutane iri uku ne, Wasu kamar guba su ke, gudunsu ake yi. Wasu kamar magani su ke, akai akai ake bukatar su. Wasu kamar abinci su ke a kullum dole ne a neme su. Yi kokari ka zama wanda a
kullum ake neman sa saboda amfanin sa.
10. Duk yadda ka yi sai wani ya zage ka. Manta da mutane kayi komai yadda ya kamata!
11. Kada ka cuci wanda ya cuce ka. Sharri kare ne, ko ya yi nisa sai ya dawo wa mai shi.
12. Duk abinda ka yi masoyin ka ne kawai ka ke burgewa. Masu hassada sai dai suyi murmushi don su batar da hankalin ka. Amma fa hassada ga mai rabo taki ce.
13. Zamo mai hakuri da bada uziri ga wanda ya yi maka ba daidai ba.
14. Kar ka damu da mai kin ka ko wanda ya ke sukar ka a rayuwar ka.
15. Kaji tsoran Allah sai ya taimake ka, kayi ma'amala da kowa bisa kyautatawa sai ka yi nasara.
*Da fatan Allah ya sa mu ci wannan Jarabawar*

1 comment: